fidelitybank

An fara kaɗa ƙuri’a a zaben shugaban kasar Chadi

Date:

An fara kaɗa ƙuri’a a zaben shugaban kasar Chadi, wani babban mataki da zai kawo karshen gwamnatin rikon kwarya ta kasar wadda ta kwashe shekaru uku.

An dai samu jinkiri wajen fara kada kuri’a, inda a wasu wuraren aka bude rumfunan zabe sa’a daya bayan lokacin da aka tsara.

Shugaban rikon kwarya Mahamat Deby ya kaɗa tasa kuri’ar a N’Djamena, babban birnin ƙasar.

Ya ce yana alfahari da cika alkawarinsa na mutunta wa’adin “zabuƙan da za su tabbatar an dawo da bin kundin tsarin mulkin kasar sau-da-kafa.”

Ya kara da cewa “Ya rage ga al’ummar Chadi su kada kuri’a kuma su zabi shugabansu da suka ga ya dace.”

Masu jefa kuri’a miliyan takwas ne ke zaben shugaban kasar daga cikin ‘yan takara 10 da suka hada da shugaban soji Deby da firaminista Succes Masra.

Ana sa ran samun sakamakon farko na zaben ne a ranar 21 ga watan Mayu, amma za a iya zuwa zagaye na biyu a watan Yuni idan har ba a samu wanda ya samu ciakkiyar nasara ba a zagayen farko na zaben.

sunnnewspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp