An fara kaɗa ƙuri’a a wasu rumfunan zaɓe a birnin Fatakwal na jihar Rivers.
A wannan karon an samu nasarar rarraba kayan aikin zaɓen a kan lokaci, saɓanin lokacin zaɓen shugaban ƙasa da ya gabata, inda masu kaɗa ƙuri’a suka yi ta jiran isar ma’aikatan zaɓe zuwa rumfunan zaɓen.
A wannan karon ma’aikatan zaɓen ne ke jiran masu kada ƙuri’a a rumfunan zaɓen, domin su fito su kaɗa ƙuri’unsu.
Rahotonni na cewa a wannan karon mutane ba su fito zaɓen ba, idan aka kwatanta da zaɓen shugaban ƙasa.