Shugaban Hukumar rarraba arziƙin ƙasa RMAFC, Mohammed Shehu, ya bayyana a Abuja cewa an fara aikin sake duba tsarin rabon kuɗaɗen shiga tsakanin gwamnatin tarayya da jihohi da kananan hukumomi.
Ya ce tun daga 1992 aka yi karo na ƙarshe, kuma dole a yi gyara domin ya dace da halin tattalin arzikin yau da kuma nauyin kowace gwamnati.
A tsarin da ake amfani da shi yanzu, gwamnatin tarayya na karɓar kashi 52.6. jihohi kuma 26.7, yayin da ƙananan hukumomi kuma ke da kaso 20.6.
Haka kuma an ware kashi 1 ga kowanne da suka haɗa da FCT da asusun muhalli da albarkatun ƙasa da kuma asusun daidaita tattalin arziki.
Shehu ya ce wannan mataki ya yi daidai da tanadin kuuɗin tsarin mulkin ƙasar, domin tabbatar da adalci da daidaito wajen rabon kuɗaɗen shiga.