An tashi canjaras a wasan farko na gasar cin kofin kwallon kafa na mata ta Najeriya tsakanin Ekiti Queens da Delta Queens.
An yi wasan ne a filin wasa na Oluyemi Kayode, Ado Ekiti.
Wasan dai ya samu halartan masoyan kwallon kafa da suka hada da uwargidan gwamnan jihar Ekiti, Mista Olayemi Oyebanji.
Sauran wadanda suka halarci bikin bude kakar wasannin akwai shugaban hukumar kwallon kafa ta Najeriya, Ibrahim Gusau, shugaban NWFL Nkechi Obi da shugaban hukumar kwallon kafa ta jihar Olu Oloworemo.
Za a buga kakar NWFL ta 2023-24 a cikin gajeriyar tsari tare da rukunin A da B wanda ya ƙunshi ƙungiyoyi 16.
A rukunin A akwai Naija Ratels, Nasarawa Amazons, Confluence Queens, Abia Angels na jihar Abia., Heartland Queens, Dannaz Ladies, Royal Queens, Adamawa Queens.
Rukunin B, yana da Delta Queens, Lakeside Queens, Rivers Angels da Sunshine Queens, FC Robo Queens, Edo Queens, Ekiti Queens na Ekiti da Bayelsa Queens.
Delta Queens sune zakarun NWFL masu karewa.


