Hukumar inshorar bankuna a Najeriya ta Nigeria Deposit Insurance Corporation (NDIC) ta ce ta fara biyan mutanen da kuɗaɗensu suka maƙale a Bankin Heritage da ya durƙushe.
Kuɗaɗen sun kai naira biliyan 46.6, kuma an fara biyan waɗanda kuɗaɗen ajiyarsu suka zarta naira miliyan biyar ne da ke da inshora.
A watan Yunin 2024 ne Babban Bankin Najeriya CBN ya karɓe lasisin Heritage, yana mai cewa mahukuntan bankin sun karya doka.
A cewar wata sanarwa daga NDIC, an fara biyan kuɗin ne daga ranar Juma’ar da ta gabata “domin tabbatar da cewa an biya dukkan masu kuɗin ajiya a bankin”.
“Kuɗaɗen da aka fara biya na abin da aka samu ne bayan sayar da kadarorin da bankin ya mallaka,” in ji sanarwar da Hawwau Gambo ta sanya wa hannu.
Ta ƙara da cewa “akwai yiwuwar kuma adadin kuɗin su ƙunshi har waɗanda aka biya masu bin bankin bashi bayan kammala biyan masu ajiya”.