Wani abin fashewa da ake tunanin bom ne ya fashe a jihar Kano, wanda ya yi sanadiyar mutuwar aƙalla mutum, sannan wasu mutum 15 suka jikkata.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa lamarin ya auku ne a ranar Asabar, wanda ya jefa tsoro da fargaba a yankin da ya faru.
Kwamishinan ƴansandan jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, wanda ya ziyarci wajen jim kaɗan bayan fashewar, ya ce abin suna tunanin fashewar daga wata mota ce da ta taso daga jihar Yobe.
“Da aka kira sai na tafi wajen cikin gaggawa, da na isa sai na fahimci cewa wani abu ne – wataƙila bom ne – ya fashe. Aƙalla mutum 5 sun rasu, sannan 15 suka jikkata,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa, “mun fara bincike asalin musabbabin aukuwar lamarin, amma muna tunanin motar da ta ɗauko abin fashewar daga jihar Yobe take.
“Binciken farko-farko ya nuna cewa wata motar tirela ce ta kwaso wasu abubuwa masu fashewa. Amma zuwa yanzu ba mu da tabbacin ko kayan sojoji ne, ko na kuma ta ƴan kwangila,” in ji shi.
“Amma za mu fayyace komai da zarar mun kammala bincike.”