Kotun sauraron kararrakin zaɓen gwamnan jihar Kaduna ta fara sanar da hukunci ta manhajar Zoom.
Tun farko an kafa majigi da kyamarori a kotun, inda daga bisani alƙalai suka bayyana ta manhajar Zoom, suka fara sanar da matsayar kotu.
Ɗan takarar gwamnan jihar a jam’iyyar PDP, Isa Ashiru ne ke ƙalubalantar nasarar gwamna Uba Sani na jam’iyyar APC.
An tsaurara matakan tsaro a harabar kotun domin gudun tashin hankali bayan sanar da hukuncin kotun.