fidelitybank

An fara ƙwato kayan abincin da aka sace a Wudil – Shugabar Ƙaramar Hukuma

Date:

Hukumomi a karamar hukumar Wudil a jihar Kano na cewa, jami’an tsaro suna ci gaba da kwato kayayyakin da wasu bata-gari suka sace a sakatariyar karamar hukumar lokacin zanga-zangar da ta rikide zuwa tarzoma.

Baya ga sace-sacen da aka yi a cikin birnin Kano cikin kananan hukumomin jihar arba’in da hudu Wudil ce lamarin tarzomar ya fi muni inda ake cewa an sace dukiya ta miliyoyin naira.

Shugabar karamar hukumar, Hajiya Bilkisu Yakubu, ta shaida wa BBC cewa, ba su da ofishoshin da za su yi aiki saboda an lalata tare da kona sakatariyar karamar hukumar.

Shugabar ta ce jami’an tsaro suna nan suna gudanar da bincike, tare da kwato wasu daga cikin kayayyakin.

Ta kara da cewa ba wai kayan gwamnati kadai aka washe ba, har ma da wasu kayayyakin na ‘yan kasuwa da sauran jama’a da aka sace.

Hajiya Bilkisu ta ce, ko kadan ba za su iya kiyasin yawan asarar da aka tafka ba a dalilin abin da masu zanga-zangar suka yi.

Haka kuma ta ce, babu wasu da za a iya fitowa fili a zarga da aikata wannan ta’asa, illa dai ta ce bincike zai gano kamar yadda jami’na tsaro suka lashi takobi, ganin yadda suke bi suna kwato wasu daga cikin abubuwan da aka sace.

vanguard newspaper nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Ƴan Jagaliya sun caka wa Matashi kuwa lokacin da ya zo karɓar naman Sallah a Kano

Matashi Ibrahim Mahmud ya rasu sakamakon caka masa wuƙa...

Kallo Ya Koma Sama: Elon Musk zai fuskanci mummunar sakamako – Trump

Ana ci gaba da takun saka tsakanin shugaban Amurka...

Zulum ya miƙa kyautar Naira miliyan 100 ga iyalan Sojojin da aka kashe

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya bai...

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...

Musulman Nijeriya a cigaba da jajircewa – Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkarshin jam'iyyar Labour a...

Akwai takaici ambaliyar Neja – IBB

Tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Babangida, ya kwatanta ambaliyar...

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...
X whatsapp