An mayar da ‘yan Najeriya 298 da suka makale a Libya gida a cikin jiragen haya daban-daban a farkon makon nan.
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta NEMA ta ce an mayar da su ne kai tsaye daga gidajen yarin Libya.
Galibin waɗanda aka mayar da su dai mata ne da suka shafe lokaci mai tsawo a sansanonin tsare mutane daban-daban a ƙasar da ta arewacin Afirka, wadda ke fama da rikici.
A cikin wadanda aka mayar gida akwai mata 119, wadanda yawancinsu suna da ciki, tare da yara mata uku da jarirai biyu, sai kuma maza 170, yara maza uku, da jariri namiji daya.
Hukumar Kula da Hijira ta Duniya (IOM) da Majalisar Dinkin Duniya (UN) ne suka dauki nauyin mayar da su gida a karkashin shirin bayar da Kariya da Taimakon bakin haure.


