Lauyan ɗan Morokon da ake zargi da sukar sarkin ƙasar a kafar sada zumunta ya ce an yanke masa hukuncin shekara biyar a gidan yari.
An tuhumi Said Boukioud da cin mutumcin gidan sarauta saboda saƙon da ya wallafa a shafinsa na Facebook a 2020, inda ya soki yadda masarautar ke alaƙa da Isra’ila.
Yana dai zaune ne a Qatar.
Kundin mulkin Maroko ya ɗora wa sarki Mohammed alhakin tafiyar da huɗɗa da ƙasashen waje, kuma duk wata suka a kansa za ta janyo hukunci mai tsanani.
Lauyan Boukioud, El Hassan Essouni, ya ce hukuncin ya yi tsauri kuma za su ɗaukaka ƙara