fidelitybank

An daure Matasan da suke kalaman batsa ta cikin Tiktok a Kano

Date:

Wata kotun majistre mai zama a Norman’s land da ke karamar hukumar Fagge na jihar Kano, ta ɗaure wasu masu amfani da shafin TikTok biyu a gidan yari, bayan samunsu da laifin amfani da bidiyo mai ɗauke da kalaman batsa.

Hukumar tace fina-finai ta jihar ta kama mutanen ne Ahmad Isa da Maryam Musa mazauna anguwar Ladanai da ke Hotoro Quarters, inda daga bisani ta miƙa su ga kotun, kamar yadda Jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Lauyan gwamnatin jihar ta Kano, Barrister Garzali Maigari Bichi, ya same su da aikata laifi da ya kunshi haɗa baki don aikata laifi da kuma wallafa hotunan bidiyo masu ɗauke da kalaman batsa a shafukan sada zumunta.

Mutanen biyu sun amsa aikata laifin.

Alkaliyar kotun, mai shari’a Hadiza Muhammad Hassan ta yanke musu hukuncin zama gidan yari na shekara ɗaya ko kuma biyan tarar naira 100,000 kowannensu – ta hore su da su zama mutanen kirki.

vanguard newspaper nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp