Wata babbar kotun jihar Oyo da ke zamanta a Ogbomoso, ta tasa keyar daya daga cikin sarakunan gargajiya a jihar zuwa gidan gyaran hali.
Rahotanni na cewa an tsare basaraken, Oloko na Oko, Oba Solomon Akinola, da wasu mutane 14 a gidan yari na Abolongo.
An tsare su ranar Laraba bisa zargin ci gaba da kai hare-hare, yunkurin kisan kai, da kuma kwace filaye.
Justice K.A. Adedokun ya ba da umarnin ne a lokacin da lauyan jihar, I. O. Abdulazeez, ya shaida wa kotun cewa wadanda ake kara sun sake kai wa mai karar Dokta Isaac Abiodun hari a kauyen Aagba.
Wadanda kotun ta tsare baya ga basaraken sun hada da Cif Sunday Aderinto, Cif Jimoh Asimiyu, Timothy Aderinto, Matthew Akintaro, Rafiu Ganiu, da Adejare Adeleru.
Sauran sun hada da Samson Ogunmola, Zachiaus Adeleru, Kamorudeen Ajibade, Raji Rasaq, Mutiu Arowosaye, Oyeyemi Oyelekan, Olusegun Oyelekan, da Sheriff Adio.
Mai shari’a Adedokun, yayin da yake magana, ya fusata kan sabon harin ta’addancin da aka kai wa Abiodun.
Alkalin kotun ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare wadanda ake tuhuma sannan ya dage sauraron karar zuwa ranar 27 ga watan Nuwamba domin sauraren neman beli.