fidelitybank

An dauke wutar lantarki a fadar Tinubu

Date:

Babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja ya gamu da matsalar ɗaukewar wutar lantarki sakamakon lalacewar wasu layikan da ke kai lantarkin sassan birnin na kamfanin da ke samar da wutar (AEDC) ya sanar.

Hatta fadar gwamnatin ƙasar matsalar ɗaukewar wutar ta shafa kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito a yau Juma’a.

Kamfanin samar da lantarkin (AEDC) a wata sanarwa da ya rinƙa fitarwa akai-akai a shafinsa na X, ya roƙi masu amfani da wutar da su yi haƙuri, yayin da ya ce ma’iakatansa na aiki tuƙuru domin shawo kan matsalar, don mayar da wutar ga sassan da abin ya shafa.

To amma daman wasu unguwannin wajen birnin kamar su Lugbe da Kubwa daman sun yi kwanaki ba su da wutar lantarkin.

A sanarwar da kamfanin ya fitar ya ambato unguwanni da yankuna da dama da matsalar ta shafa.

A jiya Alhamis aka ruwaito ministan makamashi, Adebayo Adelabu, a lokacin gabatar da shiri da manufar gwamnatin ƙasar kan samar da lantarki ya nuna takaicinsa kan ci gaba da lalacewar kayan samar da lantarki a ƙasar.

Ministan ya ɗora alhakin hakan a kan rashin aniyar kamfanonin rarraba lantarkin ta zuba jari a harkar.

labaran duniya na yau

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp