Rundunar ‘yan sandan jihar Ribas ta kama wani mutum da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ke nema ruwa a jallo tsawon shekaru hudu.
Joel Mba Okodi, wanda aka fi sani da ‘Chief,’ yana zaune ne a titin Abak, Ikot-Ekpene, jihar Akwa-Ibom.
An ce Okodi Darakta ne a Chismo Resources Limited a Ikot-Ekpene.
Wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan jihar Ribas ta fitar ta ce wanda ake zargin ya samu zunzurutun kudi har naira miliyan 50 daga hannun wani Cif Okosisi daga bisani EFCC ta kama shi.
A cewar sanarwar da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Grace Iringe-Koko ta fitar, a yayin da ake ci gaba da bincike kan almundahanar, Okodi ya tursasa abokinsa, Ochoa Okeokwu, da ya tsaya a matsayin wanda zai tsaya masa domin a ba shi beli.
Okeokwu ya mika takardun kadarorin sa, wadanda kudinsu ya kai Naira miliyan 50, a matsayin jingina a ofishin EFCC da ke Fatakwal.
Bayan beli, Okodi ya kasa gurfana a ofishin EFCC domin gudanar da bincike kuma ya kaucewa duk wata waya da aka yi masa.
A wasu lokatai da ya amsa kiran waya, ya yi ta yin barazana ga Okeokwu, inda ya gargade shi da ya daina tuntubar sa.
Hakan ya tilasta Okeokwu ya kai kara ga Sufeto Janar na ‘yan sanda, wanda daga bisani ya mika ta ga kwamishinan ‘yan sandan jihar Ribas, Olatunji Disu.
Disu, yana aiki da umarnin IGP, ya umarci jami’an Operation Sting da su tabbatar da kama wanda ake zargin cikin gaggawa.
Jami’an ‘yan sanda sun gudanar da cikakken bincike sun gano cewa wanda ake zargin yana boye a Ajegunle, Apapa, Legas.
A yayin da sanarwar ta bayyana cewa a halin yanzu hukumar EFCC na gudanar da shari’ar, Disu ya shawarci jama’a da su yi taka-tsantsan kafin su tsaya a matsayin wadanda za su tsaya masa.