Rundunar ƴan sandan Yobe ta kama wani magidanci mai shekara 43 kan zarginsa da hannu a mutuwar matarsa mai shekara 42.
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar DSP Dungus Abdulkarim ya tabbatar wa BBC faruwar lamarin wanda ya ce suna kan gudanar da bincike kan lamarin.
DSP Dungus ya ce mutumin na tare da matarsa a ɗakinsu a lokacin da aka soke ta a wuya, lamarin da ya sa ta yi ta zubar da jini har rai ya yi halinsa.
Lamarin ya faru ne a Damaturu bayan da al’ummar rukunin gidajen New Bra Bra suka tashi da labarin mai ratsa zuciya bayan gano gawar matar yashe a gidanta da yanka a wuyanta.
mai magana da yawun ‘yansandan ya ce rundunar ta fara gudanar da bincike game da mummunan lamarin domin gano mutanen da suke da hannu.
Ya kara da cewa duka da cewa yankan bai kai ga makogoron matar ba, amma ya shafi jijiyoyin da ke kai jini zuwa kanta, ta yada babu yadda za a yi ta rayu.
Ya kuma ce kawo yanzu bincikensu bai gano abin da aka yanka ta da shi ba.
A cewar rundunar, ma’auratan ma’aikata ne a jami’ar jihar Yobe da ke Damaturu.


