fidelitybank

An damke mutane 13 da hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba a Kwara

Date:

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) tare da hadin guiwar Hukumar Tsaro da Civil Defence na Jihar Kwara (NSCDC) da Hukumar Kula da Ma’adanai da Karfe ta Tarayya, sun kama wasu mutane 13 da ake zargin masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba ne da ke aiki a kauyen Kakafu a Karamar hukumar Patgi dake jihar Kwara.

Wadanda ake zargin, kamar yadda binciken THISDAY ta rawaito, an kama su ne a ranar Talatar da ta gabata a wani samame na hadin gwiwa.

An tattaro cewa an samu nasarar cafke shi ne biyo bayan sahihan bayanan sirri da hukumar EFCC ta samu kan wasu da ake zargin masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba ne da ke gudanar da ayyukansu a yankin.

Idan dai za a iya tunawa, rundunar shiyar Ilorin na EFCC da NSCDC a jihar Kwara a ranar Alhamis din da ta gabata ta kara zage damtse wajen yaki da hako ma’adinai ba bisa ka’ida ba a jihar.

Wata sanarwa da aka fitar jiya a Ilorin mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na hukumar tsaro ta farin kaya, Mista Olasunkanmi Ayeni, ta bayyana cewa: An kama wadanda ake zargin sun hada da, Buba Mohammed, Yusuf Umar, Surajo Shehu, Abubakar Abdullahi, Salisu Mohammed, Quadri Sulaiman. da Nwafor Chinonso.

“Sauran su ne: Abdullahi Isa, Mustapha Mohammed, Buhari Hassan, Basiru Jafaru, Murtala Jafaru da Jafaru Abdullahi.”

Sanarwar ta kara da cewa, an samu nasarar kwato manyan motoci biyar cike da ma’adanai daban-daban daga hannun wadanda ake zargin.

“Bincike na farko ya nuna cewa wadanda ake zargin ba sa biyan gwamnatin tarayya hakkokinsu kamar yadda doka ta tanada.”

Sai dai sanarwar ta bayyana cewa: “Ba da jimawa ba za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala binciken da ake yi.”

the sun newspaper today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

An gargadi al’umma su yi taka tsan-tsan da ambaliyar ruwan sama

Yayin da ake ci gaba da fuskantar saukar ruwan...

Gwamnatin Tarayya za ta gina hanyar sufurin jirgin ƙasa a Kano

Gwamnatin Tarayya ta ce, za ta samar da titin...

Abin da ya sa muke ci gaba da tsare Sowore – Ƴansanda

Kwamishinan ƴansanda mai kula da sashen kai ɗauki na...

INEC za ta bai wa ɗaurarru damar kaɗa ƙuri’a a lokacin zaɓuka

Hukumar zaɓen Najeriya, INEC ta ta duba yiwuwar bai...

Mai ya jawo Matan Zamfara su ka yi zanga-zanga

Ɗaruruwan mata ne tsofaffi da masu shawarya suka gudanar...

Aƙalla mutane 24,000 ne suka ɓata saboda Boko Haram a Najeriya

Kungiyar Agaji ta Red Cross ta bayyana cewa aƙalla...

‘Yansanda ku gaggauta sakin Sowore – Obi

Tsohon ɗan takarar shugaban kasa a jam'iyyar LP, Peter...

PDP ta gargaɗi mambobinta kan goyon bayan Tinubu

Babbar jam'iyyar hamayya ta PDP a Najeriya ta gargaɗi...

Mashawarcin gwamnan Kano ya rasu bayan harin ‘yan Daba

Sadiq Gentle, babban mai ba da rahoto na musamman...

An fitar da jerin sunayen Matasan ‘yan wasan da za su lashe kyautar Kopa

Masu shirya kyautar Ballon d’Or, sun fitar da jerin...

An fitar da jerin masu tsaron raga da za su lashe kyautar gwarzon bana

An fitar da sunayen wadanda za a zaba don...

Jonathan ne ya fi cancanci ya rike Najeriya Farfesa Tukur

Farfesa Tukur Muhammad-Baba, Sakataren Yada Labarai na Kungiyar Tuntuba...
X whatsapp