Ƴan sanda a Ghana sun ce sun kama wani jami’in hukumar zaɓen ƙasar da bayar da takardun kaɗa kuri’a guda 15 waɗanda aka cire sunan wani ɗan takarar shugaban ƙasa a mazaɓar Ampesika- Bayere.
Wata sanarwa da ƴan sandan suka fitar a ranar Asabar, sun ce sun kama jami’in ne mai suna Dery Joseph a mazaɓar da ke lardin gabashi na ƙasar ta Ghana, kuma suna ci gaba da gudanar da bincike.
“Muna riƙe da jami’in a halin yanzu domin ci gaba da yin bincike,” in ji sanarwar.