Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kebbi, Ahmed Magaji-Kontagora, ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan rasuwar ASP Shu’aibu Sani-Malunfashi.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan DSP Nafi’u Abubakar ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a Birnin Kebbi.
Ya ce, a ranar 19 ga watan Oktoba, ASP Abdullahi Garba, jami’i mai kula da ofishin ‘yan sanda na Sauwa, ya samu sabani da mamacin, jami’in da ke kula da laifuka na reshen Argungu.
Kakakin ya bayyana cewa, a yayin fafatawar da suka yi a gaban shagon Garba, ya caka wa Sani-Malunfashi a haƙarƙarinsa na hagu da almakashi.
Jami’in ‘yan sandan shiyya, Argungu, ya garzaya wurin da lamarin ya faru, inda ya damke jami’in da ya aikata laifin.
DPO din ya garzaya da Sani Malunfashi asibitin Sir Yahaya Memorial da ke Birnin Kebbi, inda wani likita ya tabbatar da rasuwarsa.
A yanzu haka Abdullahi Garba na tsare a hukumar binciken manyan laifuka ta jihar (CID) dake Birnin Kebbi. An kuma mika karar zuwa sashin kisan kai.
CP Magaji-Kontagora ya aika da tawagar manyan jami’an ‘yan sanda domin ta’aziyya ga ‘yan uwa da abokanan dan sandan da ya rasu. Ya kuma roki Allah Madaukakin Sarki da ya ba shi aljanna.