fidelitybank

An damƙe mutanen da suke baiwa riƙaƙen mai garkuwa da mutane a Jigawa

Date:

Rundunar ƴan sanda a jihar Jigawa, ta ce, jami’anta sun kama wani mutum mai shekara 40 da wani mai shekara 30 dukkansu a ƙaramar hukumar Gumel ta jihar bisa zarginsu da bai wa wani da ta kira riƙaƙƙen ɗan fashi da makami kuma mai garkuwa da mutane kariya.

Ɗan fashin dai ya kasance kan gaba a jerin mutanen da rundunar take nema ruwa a jallo.

Rundunar ta bayyana haka ne cikin bayanin da ta wallafa a shafinta na Facebook inda ta ce ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin ya bayyana cewa shi ne yake tuka ɗan fashin a kan babur idan ya je ƙauyen yayin da ɗayan kuma ya ce mutumin da ake nema ruwa a jallo yana kai masa hulunansa domin ya wanke su kasancewar ita ce sana’arsa.

ASP Abubakar Isah, Kakakin rundunar ƴan sandan a Jigawa ya ce an ƙara ƙaimi domin kama mutumin da ake zargi ɗan fashi ne.

Ya kuma ce yayin samamen da ƴan sanda suka kai lunguna da saƙo, an kama mutum 25 da ake zargi da kasuwancin miyagun ƙwayoyi.

Kakakin rundunar ya ce da zarar an kammala bincike a sashen binciken manyan laifuka da ke Dutse, za a gurfanar da mutanen da aka kama a kotu domin su fuskanci tuhuma.

daily post nigeria news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp