Rundunar ‘yan sandan jihar Plateau, sun ce, sun yi nasarar daƙile yunkurin garkuwa da Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Yakubu Sanda da masu garkuwa suka yi niyyar yi jiya Juma’a.
A wata sanarwa da mai magana da yawun ‘yan sandan jihar DSP Alfred Alabo ya fitar, ta ce lamarin ya faru ne lokacin da Kakakin Majalisar ya dawo gidansa da ke anguwar Federal Low-Cost a Karamar Hukumar Jos ta Kudu.
Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa wasu ‘yan bindiga guda uku sun yi niyyar shiga gidansa da ƙarfin tuwo amma sai jami’an tsaro da ke aiki suka taka musu burki.
Ya ƙara da cewa rundunar tana iyaƙar bakin koƙarinta wajen ganin ta nemo masu garkuwa da suka gudu da kuma kama su.