An dakatar da jagoran ‘yan adawa a Afrika ta Kudu, Julius Malema tare da wadansu ‘yan majalisar dokokin su biyar na jam’iyyar EFF na tsawon wata guda ba tare da albashi ba.
Kwamitin da’a na majalisar ya same su da laifin saɓa dokokin majalisa lokacin da suka jawo tsaiko a cikin watan Fabarairu lokacin da Shugaba Cyril Ramaphosa ke jawabi a majalisa.
A wancan lokacin kakakin majalisar ya bai wa jami’an tsaro umurnin su fitar da Mista Malema daga zauren majalisar.
Kwamitin na da’a ya kuma umurci ‘yan majalisar da aka dakatar su “nemi afuwar shugaban majalisar dokoki da kuma al’ummar Afrika ta Kudu saboda matsalar da suka jawo a lokacin da shugaban kasar ya ke jawabi”.
‘Yan majalisar da aka dakatar su shida, ba za su halarci zaman majalisar ba a cikin watan Fabarairu lokacin da shugaba Ramaphosa zai yi jawabinsa na gaba a zauren.
A ranar Litinin, ‘yan majalisar na jam’iyyar EFF sun ki amincewa su bayyana gaban kwamitin da’a inda Mr Malema ya nuna rashin adawarsa a fili.
“Ba zan bayyana gaban wani bature ba,” in ji Malema.