Sakataren zartarwa na hukumar kula da asibitocin jihar Kano Dakta Mansur Mudi Nagoda, ya amince da dakatar da jami’an tsaron asibitin haihuwa na Imamu Wali sannan ya umarci mahukuntan da su gaggauta diban wasu jami’an tsaron cikin gaggawa.
Hakan na kunshe ne ta cikin wata Sanarwa da jami’ar yada labarai ta Hukumar kula Da Asibitocin Jihar Kano Samira Sulaiman ta raba wa manema labarai.
Sanarwar ta kara da cewa, wannan na zuwa ne ya biyo bayan wani faifan bidiyo na wata mata mai nakuda wadda daga baya ta haihu a cikin mota sakamakon sakacin da jami’an tsaron ke yi na kulawa da marasa lafiya.
A cikin wani faifan bidiyo da ya yadu hankali a kafafan sada zumunta, an gano wani mijin majinyacin ya yi ta kwankwasa kofar asibitin ba kakkautawa, amma jami’an tsaro ba kowa cikinsu, wanda hakan ya sa mijin ya dauki hoton bidiyon faruwar lamarin ya kuma tura shi kafar sada zumunta.
Dakta Nagoda ya bayyana cewa, irin wannan lamari ya taba faruwa a ranar 26 ga watan Nuwamba, inda wata mata ta na nakuda, kuma jami’an tsaron nan ma basa nan, don haka sai mijin ya garzaya da ita asibitin kwararru na Murtala Muhammad. wanda shine mafi kusa da shi a lokacin.
Haka zalika Dr Nagoda ya amince da dakatar da wasu jami’an gwaje-gwaje su uku nan take, saboda laifukan da suka hada da sakaci, karbar kudi da kuma lalata da marasa lafiya musamman wadanda suke bukatar gwajin kuma basu da kudin biyan.
Ya bayyana cewa dakatarwar ta su ya zama dole kuma za a kafa kwamitin da zai gudanar da bincike, bin hanyoyin da suka dace, duk kuma wadanda ke da hannu a ciki za a dauki mataki kansa.
Dakta Nagoda ya koka da cewa Hukumar kula da Asibitocin Jihar Kano, ba za ta kasance a bangaren tsaro a kowane lokaci ba, ya kuma yi gargadi mai karfi ga duk wanda ya ce, “Kada wanda ya isa ya zo wurina ko wasu shugabannin hukumomi su yi ta roko, tabbas ba zan dauki sakaci ba saboda mutuncinmu yana cikin hadari. “.
Sakataren zartarwa ya ci gaba da bayanin cewa jama’a da Hukumar kula Da Asibitocin Jihar Kano ya kamata su sani cewa muna da tsarin tsaro na cikin gida don tantance kwarewar mu na asibiti da kuma da’a ta kwararru.