fidelitybank

An dakatar da Malami a jihar Neja bayan samunsa da wa’azi irin na Boko Haram’

Date:

Gwamnatin jihar Neja ta ce za ta gabatar da rahoto ga jami’an tsaro domin su ci gaba da bincike kan wani malamin addini musulunci da ta dakatar bayan zargin sa da yaɗa ‘aƙidar Boko Haram’.

Shugaban Hukumar lura da al’amuran addinai ta jihar Neja, Umar Faruk ya shaida wa BBC cewa an dakatar da malamin ne bayan binciken da gwamnatin jihar Neja ta yi a kansa.

Ya ce “kwamitin da muka kafa ya kira shi kuma mun tattauna da shi, mun gano cewa bai ma yi karatu ba.”

A cewar sa malamin na gudanar da ayyukansa a garin Tafa da ke jihar Neja, inda ya mallaki Islamiyya kuma yana da mabiya wadanda ke halartar darussansa.

“Da muka lura cewa tafiyarsa da aƙidarsa da da’awarsa akwai hatsari ga tsaron jihar Neja da tsaro na kasa, shi ne muka yanke hukuncin cewa a dakatar da shi kuma a rufe makarantarsa har sai jami’an tsaro sun yi bincike a kansa,” in ji Sheikh Faruk.

Ya ƙara da cewa malamin yana kira ne ga magoya bayan sa da su ƙaurace wa zaɓuka da duk wani abin da ya shafi dimokuraɗiyya.

hausa

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp