Hukumar kula da filayen jiragen sama ta Najeriya FAAN, ta dakatar da zirga-zirgar motocin haya a filin jirgin saman Nnamdi Azikwe International Airport (NAIA) da ke Abuja.
Abdullahi Yakubu-Funtua, Daraktan Hulda da Jama’a da Kare Kayayyakin Ciniki na Hukumar FAAN ne ya bayyana hakan kwanan nan.
Hukumar ta FAAN ta ce dakatarwar wadda ta fara tun daga ranar Alhamis, ta biyo bayan rikicin bangaran da ya barke a tsakanin masu hayar motoci a NIA.
Don haka, FAAN ta bukaci masu amfani da filin jirgin da su yi amfani da hanyoyin sufuri.
Sanarwar ta ce, “Wannan ya faru ne saboda rikicin bangaranci da ba a warware ba tsakanin masu aikin hayar mota.”