Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya amince da dakatar da dagacin garin Majidadi da ke yankin ƙaramar hukumar Akko, Mohammed Majidadi bisa zargin hannu a sace wata taransifoma.
Cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi, ya fitar, ya ce majalisar ƙaramar hukumar Akkon ta kuma dakatar da kansilan mazaɓar Kumo ta Gabas, Abdullahi M. Panda bisa wannan zargi.
A baya-bayan nan ne dai rundunar ‘yan sandan jihar ta yi holen mutanen biyu da ta ce ta kama bisa zargin haɗa baki da ɓarayi wajen sayar da taransifomar lantarkin Garin Majidadi.
Sanarwar ta ce an dakatar da mutanen biyu daga muƙamansu ne domin bayar da damar gudanar da bincike yadda ya dace.
Gwamnan jihar ya ce yana da ƙwarin gwiwa doka za ta yi aiki a kan mutanen idan aka same su da laifin da ake tuhumarsu da shi.
Gwamna ya ƙara da cewa baya ga mutanen biyu, duk wanda aka samu da hannu a sayar da taransifomar zai fuskanci hukunci. In ji BBC.