Jirgin na farko daga filin jirgin sama na Janar Tunde Idiagbon da ke Ilorin don gudanar da aikin hajjin bana na shekarar 2024 ya koma Talata 21 ga watan Mayu.
Hukumar Alhazai ta jihar Kwara ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da babban sakataren zartarwa Abdulkadir Abdulsala ya fitar a garin Ilorin a ranar Lahadin da ta gabata, inda ya ce an samu canjin ranar daga NAHCON da kamfanonin jiragen sama sakamakon wasu tsaikon da aka samu a shirin farko.
Alhazan jihar Kwara da farko an shirya yin jigilarsu na farko a ranar Litinin 20 ga Mayu, 2024.
“Abin da wannan canjin ke nufi shi ne kada alhazanmu su sake zuwa sansanin a yau (Lahadi) kamar yadda aka sanar a baya. Su zo gobe litinin 20 ga watan Mayu, gabanin kaddamar da jirgin nasu ranar Talata da karfe 10:20 na safe.
“Wannan ya shafi mahajjata ne kawai wadanda aka shirya sunayensu a farkon tashin jirgin. Za a fitar da ƙarin bayani don shiryar da dukkan alhazanmu da sauran jama’a. Yayin da ake nadama kan wannan dan canji, amma kwata-kwata ya fita daga hannun hukumar alhazai ta jiha ko kuma wata karamar hukuma,” in ji sanarwar.