Hukumar zaɓe a jihar Kaduna, ta bayyana tafiya hutu daga karɓar sakamakon zaɓen gwamnan jihar zuwa ƙarfe shida na yamma, bayan karɓar sakamakon ƙarin ƙananan hukumomi uku.
Ya zuwa yanzu an karɓi sakamakon daga ƙananan hukumomi 22 daga cikin 23 da jihar ke da su, yanzu saura ƙaramar hukuma ɗaya wadda ita ce Kudan.
Ga yadda sakamakon ƙananan hukumomin ukun ya kasance:
Karamar hukumar Kachia
APC: 23,849
LP: 1,726
NNPP: 470
PDP: 27,491
Karamar hukumar Lere
APC: 45,823
LP: 4,321
PDP: 46,36
Karamar hukumar B/Gwari
APC: 20,627
LP: 37
NNPP: 726
PDP: 19,954