Yan sanda a jihar Florida da ke Amurka, sun yi matukar kaɗuwa lokacin da suka gano cewa direban wata mota da suka tsayar a kan babbar hanya, ya kasance yaro ɗan shekara goma.
An tare yaron da ‘yar uwarsa ‘yar shekara 11 a garin Alachua da ke da nisan mil kaɗan daga inda mahaifiyarsu ta ce sun ɓace a farkon makon nan.
Ƴan sandan sun ce yaran sun tsere daga gida ne bayan da mahaifiyarsu ta ƙwace musu wayoyi.
“Mun ji mamaki da muka ga ɗan shekara goma ne yake tuka mota tare da ‘yar uwarsa,” in ji ƴan sandan.
‘Yan sanda sun kara da cewa babu wata alama da za ta nuna cewa ana cin zarafinsu a gida.
Tuni dai mahaifiyar yaran ta je garin Alachua domin kaɓar ‘ya’yanta.
Doka a Florida ta tanadi cewa sai yaro ya kai shekara 15 kafin ya iya samun izinin koyon mota, yayin da kuma sai ya kai shekara 18 kafin ya iya samun lasisin tuki. In ji BBC.