An cire wa wani sojan Ukraine makamin gurneti a ƙirjinsa wanda bai fashe ba.
Cikin hotunan da rundunar sojan Ukraine ta wallafa a shafinta na Facebook, an ga yadda abin fashewar ya kwanta kusa da zuciyar sojan a ƙirjinsa, wani hoton kuma na nuna likitan riƙe da makamin.
An yi tiyatar ba tare da amfani da salon lantarki ba na electrocoagulation – wanda aka fi amfani da shi don kare kwararar jini lokacin fiɗa – saboda “makamin zai iya fashewa a kowane lokaci”.
Sanarwar ta ce soja biyu ne suka taimaka wajen gudanar da aikin tiyatar cikin nasara.
Yanzu haka sojan yana ci gaba da murmurewa, in ji rundunar. A cewar BBC.