A yau Talala majalisar dattawa, ta ci gaba da tantance mutanen da shugaba Tinubu ya aika mata don neman amincewarta kafin naɗa su ministoci a gwamnatinsa.
Majalisar ta fara wannan aiki ne a ranar Litinin, inda ta tantance mutum 14 a tashin farko, yayin da a Talatar nan ake sa ran tantance cikon mutum 14.
Da ma dai shugaba Tinubu ya aike wa majalisar da sunayen mutum 28 ne, inda ake sa ran zai tura ƙarin wasu sunayen amma zuwa yanzu babu rahoton cewa ya aika.
A zaman na Talata, majalisar ta fara ne da tantance tsohon gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi, wanda yanzu haka shine sanata mai wakiltar mazaɓar Ebonyi ta kudu a majalisar dattawan.
Majalisar dai ta umarce shi da yin gaisuwa ya wuce ne, kamar yadda take yiwa sauran ƴan majalisar.