Majalisar dattawa, ta ci gaba da zaman tantance mutanen da shugaba Bola Tinubu ke shirin naɗawa minista.
A ranar Litinin majalisar ta fara aikin, inda ta tantance mutum 14.
Ta ci gaba da aikin a ranar Talata inda ta tantance mutum tara, sannan ta sanar da ɗage zaman ta zuwa Laraba don kammala tantance mutane biyar da suka rage.
Yanzu haka dai mutum na farko, Dele Alake ne yake amsa tambayoyi daga ƴan majalisar.
Dele Alake shi ne mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bola Tinubu.