Babbar kotun Abuja ta yi watsi da buƙatar belin da lauyoyin, tsohon shugaban Hukumar Inshoran Lafiya ta Najeriya, Farfesa Usman Yusuf.
Hukumar EFCC mai yaƙi da rashawa ce dai ta gurfanar da Farfesan bisa zargin bayar da kwangila ba bisa ƙa’ida ba a lokacin da yake jan ragamar hukumar.
Kama tsohon shugaban hukumar Inshorar ya haifar da zazzafar muhawara a ƙasar, inda wasu ke zargin bi-ta-da-ƙulli ne.
A yanzu dai kotun ta ɗage sauraron buƙatar belin zuwa ranar 27 ga watan Fabrairun da muke ciki.