Rahotanni daga Sudan na cewa ana gwabza fada a dukkan sassan babban birnin ƙasar, jim kaɗan kafin ƙarewar wa’adin tsagaita buɗe wuta na kwanaki uku, wanda ya cika da sanyin safiyar yau Laraba.
Shaidu sun ce an gwabza fada tsakanin sojojin Sudan da dakarun Rapid Support Forces (RSF) a birnin Khartoum.
Akwai kuma rahotannin amfani da makaman kaɓo jiragen yaƙi a Omdurman.
Saudiyya da Amurka ne suka shiga tsakanin domin tabbatar da tsagaita wutar na baya-bayan nan, sai dai kamar sauran lokutan baya an samu rahotannin karya yarjejeniyar.
Rikicin tsakanin sojojin Sudan da dakarun RSF ya ɓarke ne a watan Afrilun bana.


