Hukumar FA ta ci tarar Kyaftin din Portugal, Cristiano Ronaldo na wasanni biyu da kuma tarar fan 50,000 bayan da ya fasa wayar wani magoyin bayan Everton a farkon wannan shekarar.
Bayan da Manchester United ta sha kashi a hannun Everton a filin wasa na Goodison Park a kakar wasan da ta wuce, Ronaldo ya bayyana ya mari hannun wani fanti a lokacin da ya kutsa cikin rami, inda ya lalata wayar yaron.
Yanzu dai hukumar ta FA ta kammala binciken ta kuma ta ci tarar dan wasan mai shekaru 37 da haihuwa da kuma dakatar da shi, in ji jaridar The Mirror.
Ronaldo ya yarda cewa ba daidai ba ne bayan wasan da Manchester United ta buga da Everton a ranar Asabar, 9 ga Afrilu, 2022, bai dace ba.
Wata hukumar da ke da zaman kanta ta gano cewa, Ronaldon ya aikata rashin adalci da tashin hankali a yayin sauraren karar da ya biyo baya kuma ya sanya wa dan wasan takunkumin.
Wannan na zuwa ne kasa da kwana guda bayan Man United ta soke kwantiragin Ronaldo.
A halin yanzu Ronaldo yana tare da tawagar ‘yan wasan kasar Portugal a Qatar yayin da suke shirin karawa da Black Stars na Ghana a gasar cin kofin duniya da za su kara a ranar Alhamis.