fidelitybank

An ci tarar makarantar da ta wallafa hotunan dalibanta a shafin Facebook

Date:

Hukumar kula da sadarwar zamani ta Kenya ta ci tarar wata makaranta kuɗi dalar Amurka 25,000 saboda wallafa hotunan ɗalibanta a shafin intanet ba tare da samun izinin iyaye ba.

Wannan ne mataki irin haka na farko da ofishin kare bayanai ta intanet na ƙasar ya ɗauka.

Haka nan an kuma ci tarar wani gidan rawa da kuma wani kamfanin bayar da rance.

Hukumar ta ce an ci tarar gidan rawar ne bayan ya wallafa hoton wani abokin hulɗarsa a shafinsa na sada zumunta ba tare da izinin mutumin ba.

Shi kuma kamfanin bayar da rancen ya yi wa abokan hulɗarsa barazana ta hanyar kiran waya da kuma tura wa na kusa da su sakonni.

Wannan tara dai ta haifar da muhawara a ƙasar game da sirrin bayanan al’umma da kuma yadda kamfanoni ke amfani da su.

A wani saƙo da hukumar ta wallafa a shafinta na X, ta ce tana sa ran wannan tara za ta zama izina da kamfanoni domin su riƙa martaba dokokin kare bayanan al’umma, ciki har da batun neman izinin mutane kafin wallafa hotunansu a shafukan intanet.

world news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp