An ci tarar kamfanin fasaha na Meta, mai shafin Facebook da Instagram da WhatsApp, sama da yuro miliyan dubu daya sakamakon musayar bayanai daga Turai zuwa Amurka ba bisa ka`ida ba.
Kamfanin na fuskanatar tuhumar karya dokokin kare bayanan jama’a na Tarayyar Turai.
Wannan ita ce tara mafi girma da aka taba yi a karkashin dokar kare bayanan jama’a ta Turai, wadda hukumar Ireland ita ce ta yi wa kamfanin.
Bayanai sun ce an umarci kamfanin na Meta ya dakatar da aika sakonnin har tsawon watanni.
Shi kuwa ya ce zai daukaka kara kan tarar, inda kakakins Sir Nick Clegg ya ce za su bi hanyoyin shari`ar da sauran kamfanoni suke bi. In ji BBC.
Hukumar tarayyara Turai ta yi dokokin ne domin tabbatar da kare bayanan jama’a idan za a fitar da su daga Turai.
To sai dai ana fargabar cewa wadannan bayanai ba lalle ba ne su samu kariyar da ta dace a Amurka wadda ke da raunanan dokokin kare bayanan jama’a, kuma hukumomin leken asiri na Amurka za su iya samunsu.
A baya Kamfanin ya yi barazanar dakatar da ayyukansa a Turai idan ba su cimma yarjejeniyar aike sakonni cikin sauki ba.