A daren Lahadi ne wani abu ya fashe a harabar majalisar dokokin jihar Ribas.
Rahotanni na cewa wasu da ake zargi ne suka jefa abun fashewa a cikin rukunin da misalin karfe 9:25 na dare.
Lamarin ya zo ne a daidai lokacin da ake ta rade-radin cewa wasu ‘yan majalisar sun yi yunkurin tsige Gwamna Siminalayi Fubara.
A halin da ake ciki, sama da manyan motocin jami’an tsaro 17 da kuma motocin dakon kaya guda hudu na (APC), an jibge su a wurin tare da tara jami’an tsaron tarayya sama da 50 a harabar ginin.