Jami’ar Tarayya ta Gusau da ke jihar Zamfara, ta ce ya zuwa yanzu an ceto ɗalibai 14 da leburori biyu waɗanda ƴan bindiga suka sace a daren Juma’ar da ta gabata.
Wata sanarwa da hukumar jami’ar ta fitar, na cewa a jimilla, an ceto mutum 16, 14 dalibai, 2 kuma ma’aikata tun bayan faruwar lamarin.
Sanarwar ta ce ɗaliban, waɗanda suka shiga firgici a hannun ƴan bindigar, tuni aka haɗa su da iyalansu.
Haka nan sanarwar ta buƙaci ɗalibai da malaman jami’ar su ci gaba da tafiyar da lamurransu kamar yadda suka saba.
Ta kuma yaba wa dakarun Najeriya bisa ƙoƙarin da suka yi na ƙwato waɗanda aka sace.


