Hukumar da ke kula da ƴan Najeriya a ƙasashen waje, NIDCOM ta ce ta ceto mata da ƙananan yara 58 daga hannun masu safarar mutane a Ghana.
Shugabar NDICOM, Abike Dabiri-Erewa ta ce wannan na zuwa ne bayan hukumar ta samu nasarar kuɓutar da wata yarinya ƴar mai shekara 15 zuwa 16 daga hannun masu neman yin safarar ta.
Sanarwar da kakakin hukumar, Abdur-Rahman Balogun ya fitar ta ce Abike Dabiri-Erewa ta samu labarin ceto ƴan Najeriyar daga Ghana ne a lokacin da ta kai ziyara domin ganin mutanen da aka yi safara zuwa birnin Accra na ƙasar Ghana.
Sanarwar ta ce daga cikin wadanda aka ceto akwai 47 ƴan asalin jihar Kano da biyar daga Katsina da biyu daga Jigawa da kuma huɗu daga jihar Kaduna.
Balogun ya bayyana cewa a cikin wata uku jimillar ƴan Najeriya 105 kenan da aka samu nasarar ceto su daga hannun masu safara a birnin Accra.
Hukumar ta ce, ta riga ta mayar da zangon farko na mutanen ceto zuwa gida Najeriya.
Ta kuma bayyana cewa, mafi yawan waɗanda ake safarar suna faɗawa tarko ne a bisa alƙawarin za a samar masu aiki a ƙasashen waje, wanda kuma hanya ce kawai ta yaudara ba gaskiya ba.