fidelitybank

An ceto yara 12 da aka yi safararsu a jihar Abia

Date:

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta ce jami’anta sun samu nasarar ceto yara 12 da aka yi safararsu a Jihar Abia tare da ƙwato makamai da alburusai da dama a Jihar Kogi.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a shafin sada zumuntarta na X.

“A Jihar Abia, jami’anmu sun kama mutum biyu bisa zargin gudanar da gidan yara marayu ba bisa ƙa’ida ba a cikin gidansu dake kan titin Ikot Ekpene, Aba inda aka gano yara 12 daga tsakanin watanni shida zuwa shekaru 14 a cikin gidan.” in ji sanarwar

Bincike dai ya nuna cewa an yi safarar yaran ne daga ƙauyuka daban-daban a yankin Arochukwu.

“An miƙa yaran da aka ceto ga ma’aikatar harkokin mata ta Jihar Abia domin kula da su.” sanarwar ta ƙara da cewa.

“Masu laifin kuma na hannun hukuma suna fuskantar tambayoyi, kuma za a gurfanar da su a kotu bayan kammala bincike.” rundunar ta ƙar da cewa.

A wani samame kuma ta daban a Jihar Kogi, jami’an ‘yan sanda sun ce sun daƙile wata mota ɗauke da makama da alburusai da dama.

“Ana zargin wannan makamai da alaka da wani fashi da makami da aka yi kwanan nan a wajen saida man fetur a Kabba.” in ji sanarwa.

Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, IGP Kayode Egbetokun ya buƙaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da kasancewa masu lura da tsaro, kada su ba yara ga mutanen da ba su sani ba, tare da gaggauta kai rahoton duk wata motsi ko mutum da ake zargi zuwa ofishin ‘yan sanda mafi kusa.

nnn

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp