Hukumar dake Yaki da Safarar Mutane ta kasa (NAPTIP), reshen Kano, ta karbi wasu mutum 10 da aka ceto daga hannun masu safarar mutane.
Shugaban hukumar, Abdullahi Babale ne ya bayyana haka a Alhamis din nan a Kano, yayin da ya karbi wadanda aka ceto daga hannun Rundunar ‘Yan Sanda.
A cewarsa, an ceto wadanda aka yi safara ne a ranar 7 ga Disamba da misalin karfe 2:40 na yamma a wani gida da ke Unguwar Rijiyar Lemo, a wani samame da wata tawagar ‘yan sanda karkashin jagorancin CSP Bala Shuaibu suka kai yankin.
Babale ya kara da cewa, wadanda aka ceto, wanda shekarunsu ke tsakanin 22 zuwa 42, sun hada da mata 6 da maza 4, yana mai bayyana cewa “suna kan hanyarsu ta zuwa Libiya domin aikatau.”
Shugaban ya kuma yaba da taimako da hadin kan kwamishinan ‘yan sandan Jihar Kano, Salman Dogo Garba kan wannan yunkuri.
A nasa bangaren, kwamsihinan ‘yan sanda ya ce, “Za a ba wa wadanda aka ceto shawarwari yadda zasu gyaran halayensu kafin mayar da su ga iyalansu.”
Ya kuma yi kira ga iyaye da su kare ‘ya’yansu daga fadawa hannun masu safara da kan jefa su cikin bauta da sunan neman sabuwar rayuwa.