fidelitybank

An ceto Uwa da ‘ya a karkashin kasa bayan kwana biyar a Turkiyya

Date:

Duk da raguwar fatan da ake da shi na samun mutanen da suka maƙale a cikin ɓaraguzan ginin da ransu, ana ci gaba da samun abubuwa na ban al’ajabi a yankin da ake ceton waɗanda girgizar ƙasar ta rutsa da su.

Kwanaki biyar tun bayan afkuwar mummunan bala’in girgizar ƙasa da ya kai maki 7.8 a Turkiyya, har yanzu ana ci gaba da zaƙulo mutane da ransu daga cikin ɓaraguzan gini.

Wani bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta a ƙasar ya nuna lokacin da aka ceto wata mace mai ciki tare da ƙaramar ‘yarta daga cikin wani gini da ya ruguje a birnin Gaziantep na Turkiyya bayan kwashe sa’o’i 115 maƙale cikin ginin.

An dai samu rahotonnin kuɓutar da wasu mutane ciki har da wani matashi, a wasu yankunan Turkiyya bayan sa’o’i 110 maƙale cikin ɓaraguzai.

Wani bidiyo da tawagar ceto ta Jamus ta fitar ya nuna yadda aka zaƙulo wata yarinya da ranta ƙarƙashin ɓaraguzai a birnin Kahramanmaras bayan kwashe sama da sa’o’i 110.

Haka kuma hukumar jin kai ta Turkiyya ta saki bidiyon wani mutum cikin motar ɗaukar marasa lafiya, da ta kuɓutar da ransa a kusa da Kahramanmaras. In ji BBC.

the punch newspaper today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp