Rundunar ‘yan sandan jihar Anambra, ta ceto mutanen da aka sace bayan da aka yi wa ayarin ofishin Amurka kwanton bauna.
Jami’in hulda da jama’a, DSP Ikenga Tochukwu ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar da safiyar Juma’a.
“Da sanyin safiyar yau 19/5/2023, jami’an tsaro na hadin gwiwar sun ceto biyun da aka yi garkuwa da su.
Karanta Wannan: Zamu taimakawa Najeriya wajen gano wanda suka kashe ma’aikatan mu – Amurka
An cafke mutane biyu da ake zargi da kashe jami’an jakadancin Amurka
Kakakin ya kara da cewa “har yanzu ana ci gaba da wuraren da kuma za a yi karin bayani.”
An kai harin ne a ranar 16 ga watan Mayu a kan hanyar Atani/Osamela a karamar hukumar Ogbaru (LGA) ta jihar Anambra.
Tawagar ta Amurka da ta hada da jami’an Najeriya da na Amurka, sun yi wani aiki ne na kawo illar zaizayar kasa a karamar hukumar Ogbaru.
Rundunar ‘yan sandan ta ce mutane tara ne suka mutu tare da dora laifin a kan ‘yan kungiyar ‘yan asalin yankin Biafra (IPOB).
Sunan su Jefferson Obayuwane (ma’aikacin DSS mai ritaya), Sunday Prince Ubong, Ekene Nweke, Hassan Etila, Avwuvie Kaye.
Sauran wadanda suka rasa rayukansu akwai ‘yan sanda hudu: Bukar A. Kabuiki, Emmanuel Lukkpata, Friday Morgan da Adamu Andrew.
Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da cewa an tsinto gawarwakin wadanda suka mutu kuma an ajiye su a dakin ajiyar gawa.