Alhaji Abdulrazaq Nuhu Zaki, kwamishinan kananan hukumomi da masarautu na jihar Bauchi, ya tabbatar da cewa jami’an tsaro sun ceto mutane 69 da aka sace a jihar.
A cewar sa sun sako su ne a ranar Asabar.
Ya ce jami’an tsaro sun kai farmaki dajin da ‘yan fashin suka ajiye wadanda abin ya shafa.
A wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, kwamishinan ya bayyana cewa, Gwamna Bala Mohammed ya kara wa shugaban karamar hukumar, ‘yan banga, sarakunan gargajiya, jami’an tsaro da duk masu ruwa da tsaki kwarin gwiwa wajen kawar da ‘yan fashi a yankinsu.
Ya ce, Gwamna Bala ne ya jagoranci yakin da kansa, bayan da ya ziyarci wuraren da abin ya shafa, ya jajanta wa jama’a tare da karfafa musu gwiwa wajen dakile masu garkuwa da mutane.


