An samu nasarar ceto mutum 29 bayan hatsarin kwale-kwale da ya afku a jihar Sokoto, a cewar ɗan majalisar wakilai daga mazaɓar Goronyo/Gada na jihar, Bashir Gorau.
Ya ce ana fargabar akwai mutum 40 da suka ɓace kawo yanzu bayan da kwale-kwalen ɗauke da fasinjoji sama da 50 ya kife ranar Lahadi.
“Zuwa yanzu muna ci gaba da bibiyar lamarin, sannan akwai mutanen mu da suka iya ruwa da ke ƙoƙari wajen ganin sun cigaba da ceto sauran mutane. Mun ceto mutum 26 kawo yanzu,” kamar yadda ɗan majalisar ya shaida wa gidan talabijin na Channels a wata tattauna ranar Talata.
Ya kuma ce sun buƙaci hukumomin da ke kula da madatsar ruwa ta Goronyo da su rufe ruwan na tsawon kwanaki biyu don ganin ruwan ya ragu, saboda a ci gaba da aikin ceto.
Alkaluma da hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa NEMA ta fitar tun da farko, sun nuna cewa ana fargabar kusan mutum 40 ne suka rasu a hatsarin.
Sai dai, Gorau ya yi imanin cewa “babu ainihin alkaluman waɗanda suka ɓace” daga wannan mummunan hatsari.
“Hasashe ne ake yi cewa mutum 40 ko 50 sun ɓace, sai dai babu takamaimen alkaluman mutanen,” in ji ɗan majalisar.
Ya kuma koka kan yadda ake yawan samun hatsarin jiragen ruwa, inda ya ɗora laifin hakan kan rashin bn matakan kariya na shiga ruwa.