Hukumomi a jihar Sokoto sun ce, sun samu nasarar ceto mutum 25 da ransu daga cikin waɗanda suka ɓace a haɗarin kwale-kwale da ya auku a ƙauyen Kojiyo da ke ƙaramar hukumar Goronyo ta jihar.
Haɗarin ya auku ne a lokacin da mutum 50 suke hanyar tafiya babbar kasuwar Goronyo da ke Sokoto, inda tun a farko aka ceto mutum 10.
Wani kansila da ke yankin ya bayyana wa BBC cewa har yanzu ana neman sauran mutum 25.
“Mutum 50 ne a kwale-kwalen da babura 7 da wasu buhunan kayan abinci. An ceto mutum 25 zuwa yanzu, sannan ana ci gaba da neman sauran 25 ɗin,” in ji Aminu Bare.
Shugaban hukumar agajin gaggawa ta jihar Sokoto, Aminu Liman ya shaida wa BBC cewa an tura ƙwararrun masu aikin ceto domin su higa kogin domin ceto sauran waɗanda suka rage.