Hukumomin bayar da agaji sun ce, aƙalla mutum 24 aka ceto daga wani gini da ya rushe a Abuja.
Hukumoimin sun tabbatar da cewa akwai mutum uku waɗanda suka rasu sakamakon munanan raunukan da suka samu.
Karanta Wannan: Da Dumi-Dumi: An fargabar gini ya danne mutane da dama a Abuja
Ginin mai hawa uku wanda kuma aka yi shi da tsarin ginin ƙarƙashin ƙasa, ya rushe ne a ranar Alhamis a lokacin da ake ci gaba da aikin gina shi.
Babu tabbaci kan adadin mutum nawa rushewar ginin ta rutsa da su amma akasarinsu leburori ne.