Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja, NSEMA, ta tabbatar da rahoton cewa wani kwale-kwale da ke dauke da fasinjoji akalla 300 ya kife a kogin Neja da ke saman madatsar ruwan Jebba a unguwar Gbajibo da ke karamar hukumar Mokwa.
Ya bayyana cewa ya zuwa yanzu an ceto matafiya kusan 150, yayin da ake kokarin ceto sauran mutanen.
Lamarin ya faru ne a daren jiya, 1 ga Oktoba, 2024, da misalin karfe 8:30 na dare.
Hukumar a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban daraktan ta, Abdullahi Baba Arah ta ce jirgin ya taso ne daga al’ummar Mundi mai dauke da fasinjoji kusan 300.
Ya bayyana cewa matafiyan galibinsu mata ne da yara kanana domin bikin Maulidi a Gbajibo.
Shugaban hukumar ya bayyana cewa a halin yanzu hukumar NSEMA tana jagorantar aikin bincike da ceto tare da hadin gwiwar ma’aikatar sufuri ta jiha, kwamitin gaggawa na karamar hukumar Mokwa, jajirtattun ma’aikatan ruwa na cikin gida, da sauran masu aikin sa kai na al’umma.
“Duk da haka, godiya ga amsa gaggauwa daga masu aikin sa kai na al’umma; Sama da mutane 150 ne aka ceto da ransu ya zuwa yanzu.
Hukumar ta kara da cewa “har yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike da ceto domin gano karin wadanda suka tsira, kuma za a baiwa sauran jama’a karin bayani.”


