Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, ta yi nasarar fatattakar ‘yan bindiga biyar da ake zargi da yin garkuwa da su, tare da ceto mutane 100 da aka yi garkuwa da su a jihar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, ASP Abubakar Sadiq-Aliyu, ne ya bayyana hakan a Katsina ranar Juma’a yayin da yake zantawa da manema labarai nasarorin da rundunar ta samu a watan Maris.
Ya kara da cewa an kwato dabbobi 658 da aka sace, yayin da 11 da ake zargin masu kisan kai, da kuma masu fyade 29 an kama su a cikin tsawon lokacin da ake binciken.
Sadiq-Aliyua ya ce, a cikin watan Maris din da ya gabata an samu rahoton manyan laifuka guda 51 da suka hada da fashi da makami, garkuwa da mutane, kisan gilla, satar shanu da sauransu.
Ya bayyana cewa, daga cikin adadin, an gurfanar da mutane 30 da ake tuhuma a gaban kotu.
A cewarsa, an kama mutane tara da ake zargi da aikata fashi da makami, yayin da wasu 19 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban da suka hada da tsoratarwa, tunzura jama’a, sata, da kuma na gungun ‘yan bindiga.
A halin da ake ciki, rundunar a ranar Juma’a ta gabatar da chekin kudi sama da Naira miliyan 4.5 ga iyalai 13 na jami’an ‘yan sandan da suka rasu da suka rasa rayukansu a wajen aiki tukuru.
Mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, kudi da mulki, DCP Aminu Usman-Gusau ne ya gabatar da cak a madadin kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mista Aliyu Abubakar-Musa.
A cewarsa, kudaden sun fito ne daga tsare-tsaren inshorar jin dadin iyali da Sufeto Janar na ‘yan sanda domin tallafa wa iyalan ma’aikatan da suka rasu.