A ranar Talata ne wani jirgi mai saukar ungulu ya afkawa wani gini a Oba Akran Ikeja, jihar Legas.
Rahotanni na cewa, lamarin ya faru ne da misalin karfe 3:30 na yamma kusa da tashar AP Filling Station, da kuma bankin United Bank For Africa, Oba Akran.
Jirgin ya tashi da wuta a kusa da filin jirgin saman Murtala Muhammed (MMIA), inda ya nufa.
Tuni dai a ka ceto matukan jirgin su biyu da ransu.
Sai dai babu wani bayani kan ko akwai wasu fasinjoji a cikin jirgin ko a’a.
Masu ba da amsa daga Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), sun kasance a kasa a lokacin da ake gabatar da wannan rahoto.